Halin da ake ciki dangane da cutar korona a duniya

Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a kasar Madagascar
Ma'aikatan kiwon lafiya dake kula da annobar korona a kasar Madagascar RIJASOLO / AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da annobar COVID-19 ta kashe a duniya ya kai dubu 721,902 a fadin duniya ay zuwa yau asabar daga cikin mutane sama da miliyan 19 da rabi da suka harbu da cutar.

Talla

Alkaluman Hukumar sun ce har yanzu Amurka ke sahun gaba wajen yawan mutanen da suka mutu da cutar, inda take da dubu 161,358, sai Brazil mai mutane 99,572 sai Mexico mai 51,311 sannan birtaniya mai 46,511 kana India mai mutane 42,518.

Yanzu haka Yankin Kudancin Amurka ya zarce nahiyar Turai wajen yawan wadanda suka mutu da cutar, inda yake da 215,859, yayin da Turai ke da 212,794.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI