Masu dauke da Korona a Amurka sun zarta miliyan 5

Gwajin annobar korona a Dubai
Gwajin annobar korona a Dubai Karim SAHIB / AFP

Adadin wadanda suka kamu da annobar covid – 19 a kasar Amurka ya haura miliyan 5, yayin da adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya kai dubu 162.

Talla

kamar yadda kididdigar jami’ar Johns Hopkins ta nuna yau Lahadi, jummular wadanda suka harbu da cutar sunkai miliyan 5 da 603, kana dubu 162 da 441 suka mutu, nesa da duk wata kasa a duniya.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a n abaya-bayannan dai ya nuna cewa Amurkawa basu gamsu da yadda shugaban Donald Trump ke tafiyar da yaki da cutar ba, lamarin da ka iya masa illa a zaben da ke tafe na watan Nuwanba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.