Wasu ministocin Lebanon da 'yan majalisu sun bi sahun masu zanga-zanga
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministocin gwamnatin Lebanon guda biyu sun aje mukaman su tare da wasu Yan Majalisu sakamakon kazamin hadarin da kasar ta gamu da shi makon jiya wanda ya haifar da kazamar zanga zanga da kuma bukatar sauya gwamnati.
Ministocin sun hada da na yada labarai Manal Abdel Samad da na muhalli Damianos Kattar, yayin da Firaminista Hassan Diab ke bayyana shirin kira zabe nan bada dadewa ba.
Daruruwan al’ummar kasar sun yi gangami a Dandalin Mazan jiya domin nuna bacin ran su da yadda shugabannin kasar suka gaza, yayin da aka samu arangama da kuma harba hayaki mai sa hawaye a wasu sassan birnin Beirut.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu