Faransa

Faransa ta bukaci a kai zuciya nesa a Belarus

Gwamnatin Faransa ta bukaci ‘yan adawa da kuma mahunkutan kasar Belarus da su kai zuciya nesa, a daidai lokacin da ‘yan adawar ke ci gaba da tarzomar nuna rashin amincewa da nasarar da shugaba Alexandre Loukachenko ya yi a zaben da aka yi karshen mako.

Jami’an tsaro Belarus sun cafke sama da mutane dubu uku da ke zanga-zangar adawa da nasarar shugaba Loukachenko.
Jami’an tsaro Belarus sun cafke sama da mutane dubu uku da ke zanga-zangar adawa da nasarar shugaba Loukachenko. SERGEI GAPON / AFP
Talla

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar cewa, akwai bukatar kai zuciya nesa a tsakanin bangarorin biyu, lura da yadda ‘yan adawa suka fantsama kan tituna yayin da jami’an tsaro ke amfani da karfi domin tarwatsa su musamman a birnin Minsk fadar gwamnatin kasar.

Jim kadan bayan fitar da sakamakon farko da ke nuna cewa shugaba Loukachenko ya lashe zaben da 80%, abin da zai ba shi damar ci gaba da mulkin kasar ta Belarus karo na 6, ‘yan adawa sun fito fili don nuna rashin amincewa da sakamakon tare da zargin tafka magudi.

Ko baya ga birnin Minsk fadar gwamnatin kasar, an kuma samu barkewar tarzoma a birane da dama, yayin da rahotanni ke cewa jami’an tsaro sun cafke sama da mutane dubu uku. Alkaluman da mahukunta suka fitar na cewa an raunata mutane fiye da 50 da suka hada da fararen hula da kuma ‘yan sanda.

Ita ma dai gwamnatin Birtaniya ta fitar da irin wannan gargadi ga mahukuntan kasar ta Belarus, inda Ministan Harkokin Waje James Duddridge ya bukaci a kwantar da hankula, tare da samar da mafita dangane da sabanin da ya kunno kai tsakanin ‘yan adawar da kuma bangaren shugaba Loukachenko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI