Amurka

An harbe wani mahari a fadar White House

An gaggauta kawar da shugaba Donald Trump jim kadan da jin karar harbin bindiga a wajen fadar White House.
An gaggauta kawar da shugaba Donald Trump jim kadan da jin karar harbin bindiga a wajen fadar White House. Kevin Lamarque/Reuters

Jami'an tsaron da ke kare fadar shugaban Amurka sun harbe wani mutum da ke dauke da makami a wajen fadar, yayin da aka gaggauta kawar da shugaba Donald Trump daga wurin da yake ganawa da manema labarai domin kare lafiyarsa.

Talla

Tom Sullivan, babban hafsa a hukumar tsaron da ke kare shugaban, ya bayyana cewar mutumin mai shekaru 51 ya nufi wani jami’insu da ke kusa da fadar, inda ya shaida masa cewar yana dauke da makami.

Yayin da ya yi kokarin ciro makamin daga jikinsa, jami’in ya harbe shi, yayin da aka dauke shi zuwa asibiti.

Yayin da lamarin ke faruwa, jami’an hukumar sun dauke shugaba Trump daga dakin da yake ganawa da manema labarai.

Daga bisani shugaba Trump ya koma dakin taron inda ya shaida wa manema labari abin da ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.