Rasha-WHO

WHO na duba yiwuwar amincewa da riga-kafin Rasha

Masana kimiya na ci gaba da kokarin samar da riga-kafin cutar coronavirus
Masana kimiya na ci gaba da kokarin samar da riga-kafin cutar coronavirus Alexander Ryumin\TASS via Getty Images

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa, duk wani riga-kafin Covid-19 da ta amince da shi, sai an yi cikakken nazari a kansa domin sanin illarsa. Wannan na zuwa ne bayan Rasha ta sanar da fara amfani da wani sabon riga-kafin cutar.

Talla

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce, kasarsa ta zama ta farko a duniya da ta amince da bayar da riga-kafin cutar coronavirus.

Mai Magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya, Tarik Jasarevic ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa, yanzu haka hukumar ta WHO na tuntubar hukumomin Rasha kuma ana kan gudanar da tattaunawa game da yiwuwar amincewa da riga-kafin.

Jami’in ya ce, kafin riga-kafin ya samu karbuwa, sai an yi cikakken nazari a kansa domin tabbatar da rashin illarsa da kuma ingancinsa.

Cibiyar bincike ta Gamaleya ce ta kirkiri riga-kafin mai suna Sputnik V tare da hadin guiwar ma’aikatar tsaron Rasha.

Jumullar riga-kafin cutar coronavirus 165 ake fafutukar samar da su a sassan duniya kamar yadda Hukumar Lafiya ta WHO ta sanar a baya-bayan nan.

Daga cikin wannan adadi, 139 na a matakin farko a dakunan binciken kimiya, yayin da 26 suka kai matakin fara gwajin su kan bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.