Coronavirus

Za mu samu galaba kan coronavirus-WHO

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta hakikance cewa, tana da kwarin guiwar samun galaba kan annobar coronavirus wadda ta doshi lakume rayukan mutane dubu 750, tare da harbar kimanin miliyan 20 a sassan duniya.

Talla

Hukumar Lafiyar  ta ce, har yanzu ba a makara ba wajen daukar matakan da suka dace domin hana yaduwar cutar ta Covid-19.

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce, a cikin wannan makon, adadin masu dauke da coronavirus zai kai miliyan 20, sannan kuma mamata za su kai dubu 750.

Ghebreyesus ya kara da cewa, akwai babbar damuwa dangane da wadannan alkaluma domin kuwa duk wani rai da aka rasa nada muhimmanci a cewarsa.

Sai dai shugaban na WHO ya ce, akwai alamun samun nasara kuma ba a makara ba wajen magance annobar ta coronavirus, inda ya bada misali da kasashen da suka yi nasarar dakile cutar da suka hada da New Zealand da Rwanda, yayin da ya jinjina wa kasashen da cutar ta yi wa mummunan kamu amma kuma a yanzu suka dukufa wajen magance ta a cikin gida.

A cewar shugaban na Hukumar Lafiyar ta Duniya, za a iya bude kasashe domin ci gaba da harkoki muddin aka yi nasarar dakile cutar wadda ta lakume rayukan mutane dubu 731 da 500 ya zuwa tsakar ranar jiya Litinin, sannan ta harbi kusan miliyan 19.9 tun bayan barkewarta a cikin watan Disamban bara a China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI