Amurka

Biden da Harris sun yi wa Trump luguden caccaka

Dan takarar shugaban kasa a Jam’iyyar Democrat Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris sun yi wa shugaban Amurka Donald Trump luguden caccaka, inda suka bayyana shi a matsayin mara kwarewa wanda kuma ya fatattaka Amurka.

Joe Biden da Sanata Kamala Harris
Joe Biden da Sanata Kamala Harris Reuters
Talla

‘Yan takarar biyu sun gudanar da yakin neman zaben su a tare, kwana guda bayan Biden ya zabi Harris a matsayin mataimakiyarsa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cece-kucen da Amurkawa ke yi game da zaben Harris a matsayin mataimakiyar Biden

Tattaunawa tare da Alhaji Sulaiman Garba Krako Saminaka kan Kamala Harris a Amurka

A martaninsa, shugaba Donald Trump ya ce, Mis Harris ta ‘duro daga sama tamkar tsauni’ a kokarinta na neman kujerar mataimakiyar shugaban kasa.

Mista Biden wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne, zai fafata da Trump a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Biden da Harris sun gudanar da yakin neman zabensu a bayan-fage a Wilmington Delaware saboda annobar coronavirus, yayin da suka dare kan dandamali sanye da kyallen rufa baki da hanci domin yi wa tawagar ‘yan jaridu jawabi.

A yayin jawabinsa, Biden ya bayyana cewa, babu abin da Trump ya iya face kururuwa, saboda abin da ya fi kwarewa kenan.

“Ba abin mamaki ba ne, saboda kururuwa ita ce abin da Donald Trump ya fi kwarewa fiye da duk wani shugaban kasa a tarihin Amurka” inji Biden.

A yayin jawabinta, Harris ta bayyana cewa, cutar coronavirus ta yi wa Amurka mummunar illa ce saboda sakacin shugaba Trump.

Kimanin mutane 75 sun yi dandazo a wajen dakin yakin neman zaben duk da yayyafin ruwan sama da ke sauka domin gane wa idanunsu ‘yan takarar biyu kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya rawaito.

Sanata Harris ta California, ita ce mace ta farko bakar fata da ta tsaya takarar mataikamiyar shugaban kasa karkashin wata babbar jam’iyya a Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI