Sauyin yanayi

Dumamar yanayin itatuwan kurmi na da illa-Bincike

Dumamar yanayin itatuwan kurmi na da illa daidai da illar dumamar yanayin da gurbatacciyar hayakin da masana'antu ke fitarwa
Dumamar yanayin itatuwan kurmi na da illa daidai da illar dumamar yanayin da gurbatacciyar hayakin da masana'antu ke fitarwa AFP PHOTO / Ezequiel BECERRA

Wani sabon rahoton binciken masana yanayi da aka fitar a birnin Paris na Faransa na cewa dumamar yanayi da ake samu daga itatuwan yankunan kurmi ko fadama na da illar gaske kamar wadda ake samu daga masana'antu da ababan hawa.

Talla

Masanan karkashin jagorancin Andrew Nottingham na Jamiar Edingburg ya shaida wa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa, sabanin hasashen da aka dade da amincewa, yanzu masanan na ganin tururin da matattun itatuwa da busassun ganyen itatuwa ke fitarwa na taka rawa wajen kara dumamar yanayi.

A cewar masanan, iskar da matattun itatuwa da busassun ganyaye ke fitarwa a fadin duniya ya kusan ninka wanda ayyukan bil'adama ke haifar da shi har sau 10, wajen kara dumamar yanayi.

Masanan sun gudanar da gwaje-gwaje da dama, inda suke hasashen cewa idan har aka samu zafin kasa a kurmi da ya kai ma'auni 4 na Celcius na tsawon shekaru 2, wani lokaci a shekara ta 2100 na iya haifar da ton biliyan 65 na Carbon wanda kenan ya kai kusan ton biliyan 240 na iskar da halittun ke fitarwa a sararin subihana.

Wannan kuma a cewar masanan ya nuna kenan an samu har ninki 6 idan aka kwatanta da gurbataccen iska wanda ake ganin ayyukan bil'adama ke haifarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.