Isra'ila zata dakatar da shirin mamaye matsugunin Falasdinawa - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump da wasu mukarrabansa
Shugaban Amurka Donald Trump da wasu mukarrabansa REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikin sa na samun nasarar kulla yarjejeniyar huldar diflomasiyar tsakanin Israila da Kasar Daular Larabawa.

Talla

A jawabin da ya yiwa manema labarai, Trump ya bayyana kulla sabuwar huldar kasashen a matsayin gagarumar nasara tsakanin manyan kawaye biyu, yayin da ya kuma sanar da dakatar da mamaye Yankunan Falasdinawa da Israila ke shirin yi.

Shugaban yace nan gaba kadan za’a samu Karin kasashen Musulmin da zasu kulla yarjejeniyar diflomasiya da Israila.

Tuni Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya bayyana yau a matsayin ranar tarihi, yayin da Yariman Daular Larabawa ya tabbatar da yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.