Sama da mutane dubu 750 korona ta kashe a Duniya

Ma'aikatar lafiya da ke binne gawan masu dauke da korona a Brazil
Ma'aikatar lafiya da ke binne gawan masu dauke da korona a Brazil REUTERS/Pilar Olivares

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a duniya ya zarce dubu 750,000 ya zuwa tsakiyar ranar yau Alhamis, bayan annobar ta Kama mutane sama da miliyan 20 a fadin duniya.

Talla

Alkaluman Hukumar sun nuna cewar yanzu haka Kudancin Amurka da Yankin Carribean suka fi jin radadin cutar, ganin yadda ta kashe mutane dubu 228,572.

Hukumar tace kusan rabin mutanen da suka mutu a duniya sun fito ne daga cikin kasashe 4 kacal da suka hada da Amurka mai mutane dubu 166,038 sai Brazil mai mutane dubu 104,201 sai Mexico mai mutane dubu 54,666 sannan India mai mutane dubu 47,033.

Rahotanni sun bayyana cewar a cikin mako guda mutane dubu 18,600 sun mutu a kudancin Amurka da Carribean wanda ya zarce 8,000 da aka samu a kasashen Amurka da Canada da 7,600 da aka samu a Asia da kuma kusan 2,700 da aka samu a Afirka, yayin da aka samu 2,600 a nahiyar Turai.

Hukumar ta kuma ce wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a Afirka yanzu haka sun zarce miliyan guda, kuma sama da dubu 24 daga cikin su sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.