Lebanon

UNESCO na jagorantar sake gine wuraren tarihi a Lebanon

Akalla gine-gine dubu 8 suka ruguje a sanadiyar fashewar sinadirai a birnin Beirut
Akalla gine-gine dubu 8 suka ruguje a sanadiyar fashewar sinadirai a birnin Beirut REUTERS/Aziz Taher

Hukumar Bunkasa Ilimi, Kimiya da Tattalin Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta lashi takobin jagorantar fafutukar kare wuraren tarihin da ke fuskantar barazana a Lebanon bayan aukuwar ibtila’in fashewar sinadarai a birnin Beirut.

Talla

Hukumar UNESCO ta gargadi cewa, gine-ginen tarihi 60 na fuskatar barazanar rugujewa.

Rugugin fashewar, sai da ya karade sassan birnin Beirut, amma Gemmayzeh da Mar-Mikhael da ke makwabtaka da tashar jiragen ruwan da fashewar ta auku, sun fi jin jiki kuma wadannan wurare biyu na dauke da dimbin gine-ginen tarihi.

Mataimakin Darekta Janar a Hukumar UNESCO, Ernesto Ottone ya bayyana cewa, kasashen duniya sun aike da kwararan sakwannin goyon baya ga Lebanon jim kadan da aukuwar ibtila’in.

Babban Jami’in ya ce, UNESCO ta dukufa wajen jagorantar mayar da martani a bangaren al’adun kasar wanda za a sake ginawa.

Shugaban Sashen Kula da Kayayyakin Tarihi a Ma’aikatar Al’adu ta Lebanon, Sarkis Khoury ya bayyana cewa, fashewar sinadaran ta yi illa ga akalla gine-gine dubu 8 kuma 640 daga cikinsu na da dimbin tarihi, yayin da kimanin 60 daga cikinsu ke fuskantar barazanar rugujewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.