Isra'ila-Falasdinu

Dambarwa ta mamaye yarjejeniyar Isra'ila da Daular Larabawa

Falasdinawa na zanga-zangar adawa da yarjejeniyar Isra'ila da Daular Larabawa
Falasdinawa na zanga-zangar adawa da yarjejeniyar Isra'ila da Daular Larabawa REUTERS/Mohammed Salem

Shugabannin kasashen duniya na fatar yarjejeniyar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta cimma da Isra’ila za ta farfado da tattaunawar zaman lafiya a yanki Gabas ta Tsakiya duk da cewa Falasdinawa sun bayyana matakin a matsayin yaudara.

Talla

A karo na uku kenan da Isra’ila ke kulla makamanciyar wannan yarjejeniya mai cike da tarihi da Hadaddiyar Daular Larabawa,

Ana sa ran karkashin wannan yarjejeniya, Isra’ila za ta jingine shirinta na mamaye yankunan Falasdinawa, matakin da Kungiyar Tarayyar Turai da wasu kasashen Larabawa suka yi madalla da shi.

Sai dai a martanin da ta mayar kasar Iran ta soki matakin wanda ta kira ‘shashanci’, yayin da gwamnatocin kasashen Masar da Oman da Bahrain suka goyi bayan yarjejeniyar.

Sai dai Falasdinawa sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin, inda suka kona hotunan shugabannin kasashen na Larabdawa da suka goyi bayan shirin a birnin Nablus da ke yankin Yamma ga Kogin Jordan.

Shugabannin Falasdinawan sun bayyana yarjejeniyar a matsayin yaudara, suna masu cewa, za su janye jakadansu daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kawo yanzu Saudiya wadda ke zama jagora a yankin Gabas ta Tsakiya ba ta ce uffam ba dangane da wannan dambarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.