Amurka-Iran

Trump ya lashi takobin kawo rudani a takunkumin Iran

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump AP Photo/Alex Brandon

Shugaban Amurka Donald Trump ya lashi takobin amfani da wata dabara mai cike da rudani domin maido da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya kan Iran, matakin da zai yi gagarumar illa ga yarjejeniyar nukiliyar da mahukuntan Tehran suka cimma da manyan kasashen duniya.

Talla

Shugaba Trump ya bayyana haka ne kwana guda bayan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi watsi da kudirin Amurka na tsawaita takunkuman hana cinikayyar makamai da Iran.

A yayin taron manema labarai a filinsa na kwallon lambu da ke New Jersey, shugaba Trump ya ce, za su waiwayi baya, yana mai cewa, za a ga abin da zai wakana a cikin wannan mako.

Trump na magana ne dangane da muhawarar nan mai sarkakiya da ake tafkawa da ke cewa, har yanzu Amurka na cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015 duk da cewa, shugaban ya janye kasar daga cikinta.

Yanzu haka Trump zai yi amfani da wannan dama don yin matsain lamba don ganin cewa, an maido da takunkumai kan Iran muddin aka same ta da karya sharuddan yarjejeniyar nukilyarta.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, Amurka ta gaza soke abin da ya kira yarjejeniyar da ke cikin halin mutu-kwa-kwai rai-kwa-kwai da suka cimma da manyan kasashen duniya, abin da ya sa Tehran ta samu sassaucin takunkuman da aka kakaba mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.