Lebanon ta gindaya sharudan sulhu da Isra'ila

Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun yayin ganawa da jami'in gwamnatin Amurka
Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun yayin ganawa da jami'in gwamnatin Amurka Dalati Nohra/Handout via REUTERS

Shugaban Lebanon Michel Aoun, ya ce a shirye kasarsa take ta zauna lafiya da Isra’ila, amma fa dole sai kasashen biyu sun warware matsalar da ke tsakaninsu kafin a kai ga matsayin sulhu.

Talla

Wannan furucin na shugaban Lebanon a ganawarsa da wata tashar talabijin ta kasar Faransa, na nuni da cewa mai yiwuwa kasar wacce kawa ce ga Hezbollah ta bar kofa a bude don samun fahimtar juna da Isra’ila.

An shafe gwamman shekaru ana cikin hali na rashin jituwa tsakanin Lebanon da Isra’ila, inda jifa jifa rikici na barkewa tsakaninsu a kan iyaka, ta kudancin Lebanon, inda kungiyar Hezbollah ke da iko.

Kalaman na shugaba Aoun na zuwa ne bayan sanarwar maido da danganta tsakanin Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa, kasar Larabawa ta 3 kacal da ke cikakken huldar diflomasiyya da Isra’ila tun da aka kirkiro ta a shekarar 1948.

Akwai daddadiyar hadaka ta siyasa a tsakanin jam’iyyar Aoun ta Christian Free Patriotic Movement da kungiyar with Hezbollah da ba ta ga maciji da Isra’ila, lamarin da ya bata karfin kasancewa mai rinjaye a majalisar dokokin kasar da gwamnatin da ta yi murabus a makon da ya gabata biyo bayan fashewar sinadarai a babban birnin kasar Beirut.

A Juma’ar da ta gabata shugaban Hezbolah Hassan Nasrallah ya caccaki sabuwar dangantara Isra’ila da Hadaddiyar Daular Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.