Rasha na shirin tura dakarunta zuwa Belarus
Dubun dubatar magoya bayan ‘yan adawa ne suka gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da Alexander Loukachenko a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi a kasar Belarus.To sai dai yayin da Tarayyar Turai da Amurka ke ci gaba da nuna goyon bayansu ga ‘yan adawar, a nata bangare Rasha ta ce a shirye take ta tura sojoji domin kare shugaban kasar idan bukatar hakan ta taso.
Wallafawa ranar:
Mutanen da aka bayyana cewa adadinsu ya kai dubu 100 zuwa dubu 200 ne suka fito don gudanar da zanga-zangar a birnin Minsk da sauran sassan na kasar ta Belarus a jiya lahadi, a daidai lokacin da Alexander Loukachenko ke ci ga da bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi a kasar.
Masu zanga-zangar wadanda mafi yawansu ke sanye da fararen tufafi, sun rika rera wakoki da a ciki suke kira ga shugaba Loukachenkao ya sauka daga karagar mulki, kafin daga bisani su yi cincirindo a dandalin tunawa da wadanda suka kwanta dama a lokacin yakin duniya na biyu da ke tsakiyar birnin Minsk.
To sai dai yayin da ‘yan adawa ke gudanar da zanga-zangar, a nasu bangare magoya bayan shugaban na can suna gudanar da nasu gangami don jaddada goyon bayansu a gare shi.
A jawabi da ya gabatar wa magoya bayansa, shugaba Loukachenko ya sa kafa ya yi fatali da bukatar ‘yan adawar da ke neman a gudanar da sabon zabe, inda ya zargi abokiyar hamayyarsa ta siyasa Svetlana Tikhanovskaia a matsayin wanda ke kare muradun kasashen ketare.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu