Trump na shirin yin ahuwa ga mutumin da ya bada asirin Amurka

Tsohon jami’in leken asirin Amurka Edward Snowden
Tsohon jami’in leken asirin Amurka Edward Snowden France24

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce yana tunanin yi wa tsohon jami’in leken asirin kasar Edward Snowden afuwa, wanda ya samu mafaka a Rasha tun shekara ta 2013 bayan da mahukuntan Amurka suka bayar da sammacin kama shi saboda fallasa bayanan sirrin kasar.

Talla

Trump, wanda ke zantawa da jaridar New York Post, ya ce a gaskiya akwai mutane da dama da ke ganin cewa ba a yi wa Snoden adalci ba, saboda haka zai yi dudi dangae da yiyuwar yi masa afuwa.

Amurka ta zargi Rasha wajen taimakawa Snowden tserewa wanda aka ruwaito ya kaucewa hawa jirgi zuwa Cuba daga Rasha don gudun kada a cafke shi.

Bayan da  ya yi batan dabo a Rasha, amma shugaban Wikileaks Julian Assange yace Snowden yana cikin koshin lafiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.