Lebanon

Na gamsu da hukuncin kisan mahaifina-Hariri

Saad Hariri
Saad Hariri REUTERS/Mohamed Azakir

Tsohon Firaministan Lebanon Saad Hariri ya amince da hukuncin kotun duniya dangane da kisan mahaifinsa Rafik Hariri da  aka yi a shekarar 2005, wanda kotu ta bayyana samun wani dan kungiyar Hezbollah Salim Ayyash da aikata kisan.

Talla

Yayin da yake mayar da martani bayan hukuncin, Saad Hariri ya ce a matsayinsa na mai magana da yawun iyalan Hariri da sauran mutanen da aka kashe sun amince da hukuncin.

Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta samu Salim Ayyash na kungiyar Hezbollah da laifin kai harin da ya hallaka Rafik Hariri da kuma tarin magoya bayansa a shekarar 2005.

Ayyash mai shekaru 56 bai samu damar zuwa kotun ba, yayin da kotun ta wanke wasu mutane 3 Assad Sabra da Hussein Oneissi da Hassan Habib Merhi saboda kwararan shaidu.

Alkalan kotun sun kuma ce babu wata shaidar da ke nuna hannun Syria wajen aikata kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.