Amurka

Democrat ta amince wa Biden ya kara da Trump

Joe Biden
Joe Biden AP Photo/Carolyn Kaster

'Yan Jam’iyyar Democrat a Amurka sun amince a hukumance da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya zama dan takarar da zai kalubalanci shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba.

Talla

Wakilan Jam’iyyar daga jihohin Amurka 50 da yankunanta 7 duk sun amince da takarar Biden lokacin da aka kira sunayensu ta waya sakamakon annobar korona.

Biden ya bayyana farin cikinsa da goyan bayan da ya samu, yayin da ake sa ran a ranar Alhamis ya gabatar da jawabin amincewa da karbar takarar.

Cikin fitattun Amurkawan da suka yi wa taron jawabi ta bidiyo sun hada da tsohon shugaban kasa Jimmy Carter da Bill Clinton da John Kerry da Michelle Obama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.