MDD

MDD ta jinjina wa ma'aikatan agaji na duniya

Wasu daga cikin ma'aikatan agaji masu yaki da cutar coronavirus
Wasu daga cikin ma'aikatan agaji masu yaki da cutar coronavirus Pierre-Philippe Marcou / AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta jinjina wa ma’aikatan agaji da ke yaki da annobar korona, a daidai lokacin da suke fuskantar karin hare-hare daga sassan duniya.

Talla

Ofishin Jinkai na Majalisar ya ce yayin da yau ake tuna rawar da irin wadannan jami’ai ke takawa a duniya, a shekarar 2019 ma’aikatan agaji 125 aka kashe a hare hare daban daban, yayin da aka raunata wasu daruruwa ko kuma aka sace wasu.

Alkaluman hukumar sun ce, sau 277 aka kai wa ma’aikatan agaji 483 hari, 125 sun mutu, 234 sun samu raunuka, yayin da aka yi garkuwa da 124.

Sanarwar Majalisar ta ce, an fi samun yawancin hare-haren ne a kasashen Syria sai Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Afghanistan da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya ce, aiki ya yi wa jami’an agajin yawa ganin yadda suke fama da annobar COVID-19 da kuma wasu rikice-rikice da suka addabi kasashen duniya.

Majalisar ta bayyana damuwa kan kazamin harin da aka kai yan kwanakin nan a Jamhuriyar Nijar da Kamaru, inda aka kashe ma’aikatan agajin, kuma aka jikkata wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.