Saudiya

Ba za mu yi hulda da Isra'ila ba-Saudiya

Ministan Harkokin Wajen Saudiya, Faisal bin Farhan tare da takwaransa na Jamus Heiko Maas a birnin Berlin.
Ministan Harkokin Wajen Saudiya, Faisal bin Farhan tare da takwaransa na Jamus Heiko Maas a birnin Berlin. John MacDougall/Reuters

Saudiya ta ce ba za ta bi sawun Hadaddiyar Daular Larabawa wajen kulla huldar Diflomasiya da Isra’ila ba, har sai kasar ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhunta rikicinta da Falasdinawa wadda kasashen duniya ke goyon baya.

Talla

A makon jiya Hadaddiyar Daular Larabawa ta zama kasar Larabawa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya da ta dawo da huldar diflomasiya tsakaninta da Isra’ila, abin da ake ganin zai bude kofa ga karin kasashen na Larabawa wajen gyara alakarsu da Isra’ilar ciki har da Saudiya.

Sai dai bayan shafe kwanaki ba tare da cewa uffam ba kan lamarin duk da fuskantar matsin lamba daga Amurka, Saudiya ta hannun Ministan Harkokin wajenta Yarima Faisal bin Farhan da ke ziyara a Jamus, ta ce ba za su maido da huldar Diflomasiya da Isra’ila ba har sai ta rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen rikicinta da Falasdinawa da kasashen duniya suka amince da ita.

Kalaman Yarima Faisal dai na a matsayin martanin Saudiya na farko kan matakin Hadaddiyar Daular Larabawa na sake kulla yarjejeniya da Isra’ila, kasar Larabawa ta uku da ta yi hakan, bayan Masar da kuma Jordan.

Yayin ganawa da manema labarai a birnin Berlin, Yarima Faisal tare da takwaransa Ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas, ya caccaki Isra’ila kan yadda take gaban kanta wajen mamaye karin yankunan Falasdinawa a gabar yammacin kogin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.