Rasha

An dirka wa jagoran 'yan adawar Rasha guba

Alexei Navalny
Alexei Navalny REUTERS/Tatyana Makeyeva/File Photo

Jagoran ‘yan adawar Rasha, Alexei Navalny na cikin halin rai-kwa-kwai-mutu-kwa-kwai a wani asibiti da ke Siberia bayan an sanya masa guba a shayinsa kamar yadda mai magana da yawunsa ta bayyana.

Talla

Navalny mai shekaru 44 kuma lauya da ke yaki da cin hanci da rashawa, na cikin manyan masu sukar lamirin shugaban Rasha, Vladimir Putin.

Mai magana da yawunsa, Kira Yarmysh ta ce, an kwantar da Navalny a sashin kula da marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali a asibitin birnin Omsk na Siberia bayan ya shide a cikin jirgin saman da ya dauko shi daga birnin Moscow, lamarin da ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa.

Yarmysh ta ce, da gangan aka bai wa jagoran ‘yan adawar na Rasha guba, yayin da likitan asibitin Alexander Murakhovsky ya ce, yana cikin mawuyacin hali.

Rahotanni sun ce, jami’an tsaro da masu bincike sun halarci asibitin domin yi wa likitan tambayoyi game da Navalny.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.