Iran

Iran ta sanar da kera makamai masu linzami duk da matsin lambar Amurka

Shugaban Iran Hassan Rohani.
Shugaban Iran Hassan Rohani. © AFP

Kasar Iran ta sanar da samun gagarumar nasarar kerar wasu makamai masu linzami guda biyu dake iya tafiyar kilomita 1,400 duk da sukar da Amurka ke yiwa kasar na ganin tayi watsi da kere keren.

Talla

Ministan tsaron Iran Amir Hatami yace daya daga cikin makaman da ake harba shi daga kasa zuwa sama, kuma yake cin zangon kilomita 1,400 an sanya masa suna Qaseem Soleimani domin karrama tsohon kwamandan sojin da Amurka ta kashe, yayin dayan kuma mai cin kilomita 1,000 aka masa suna Abu Mahdi.

An dai nunawa jama’ar kasar makaman guda biyu ta kafar talabijin wadanda aka ce an hada su ne a cikin gida domin inganta tsaron kasar.

Kasar Amurka ta kashe Janar Soleimani da Abu Mahdi al-Muhandis a watan Janairu lokacin da suke ziyarar kasar Iraqi.

Tuni gwamnatin Iran ta bada umurnin kamo mata shugaba Donald Trump saboda kashe hafsoshin guda biyu domin gurfanar da su gaban shari’a saboda aikata kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.