Turai-Iran-Amurka

Turai na shirin juya baya ga sabbin takunkuman Amurka kan Iran

Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen.
Shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen. Photo: Kenzo Tribouillard/AFP

Amurka ta kaddamar da shirin sake sabunta takunkumai a kan kasar Iran, duk da ya ke alamu sun nuna yiwuwar kasashen Turai su juya baya ga sabon yunkurin.

Talla

Amurka dai ta fusata sakamakon yadda kasashen na Turai ke nuna rashin amincewa da yunkurin sake dawo da takunkuman kan Iran, inda sakataren harkokin waje Mike Pompeo ya fito fili karara ya zargi Faransa, Birtaniya da kuma Jamus a matsayin wadanda ke yi wa shirin nata kafar angulu.

Pompeo, wanda ya yi tattaki zuwa birnin New York, ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, Iran ta karya yarjeniyar da ta sanya wa hannu da kasashen duniya a game da shirinta na nukiliya a 2015, saboda haka dole ne a lafta wa kasar takunkuman hana saye ko kuma sayar da makamai.

To sai dai kasashen na Faransa, Birtaniya da Jamus, sun ce Amurka ba ta da hurumin tsoma baki a game da duk wani zance da ya shafi yarjeniyar nukiliyar kasar Iran, domin kuwa Amurka ta janye daga yarjejeniyar tun a shekara ta 2018.

Bayan darewarsa ne a kan karagar mulki, shugaba Donald Trump ya yanke shawarar janyewa daga wannan yarjejeniya, tare da yin kira ga sauran kasashen da suka sanya ma ta hannu, wato Faransa, Birtaniya, Jamus, Rasha da kuma China da su ma su dauki irin wannan mataki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.