Maharin Masallacin birnin Christchurch ya gurfana gaban Kotu
Mai tsatsauran ra’ayin wariyar launin fatan nan da ya kashe Musulmai 51 lokacin da suke tsaka da sallah a wani masallacin kasar New Zealand ya gurfana gaban kotu a yau Litinin, amma babu alamun nadama a tattare da shi, yayin da wadanda suka tsallake rijaya da baya daga hatsarin suka tinkare shi a kotun.
Wallafawa ranar:
Masu gabatar da kara a kotun da ke birnin Christchurch sun gabatar da bayanai masu rikitarwa na yadda maharin, Brenton Tarrant ya kitsa harin da ya lakume rayuka, da kuma yadda ya so da ya salwanta rayukan da suka zarta haka.
Dan bindigan, wanda dan asalin Australia ne, ya yi tozali da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, inda wadanda suka tsallake rijiya da baya yayin farmakin nasa suka bayyana yadda suka saje da gawarwaki a lokacin da Tarrant ya afka musu, da kuma yadda har yanzu suke jin karar bindiga mai sarrafa kanta.
Kotun ta saurari yadda a ranar 15 ga watan Maris Tarrant wanda ya yi damara da manyan makamai ya bude wuta a kan maza da mata da yara dake ibada a masallatai, ba tare da ya saurari magiyar da suke mai ba.
Tarrant ya amsa zarge zarge har guda 51 da ya da ake mai, da suka hada da na ta’addanci a masallatai biyu da ke birnin Christchurch.
Sanye da kayan gidan yari a tsakiyar ‘yan sanda 3 Tarrant ya yi ta raba idanuwa yana kallon dakin kotun, yayin da ake bayar da bahasi masu ratsa jiki.
Masu gabatar da kara dai na fatan Tarrant mai shekaru 29, ya kasance mutum na farko da za a yi wa daurin rai da rai sakamakon irin wannan laifi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu