Amurka

Kamfanin TikTok ya maka Donald Trump a Kotu

Tambarin kamfanin TikTok.
Tambarin kamfanin TikTok. REUTERS/Dado Ruvic

Kamfanin TikTok ya sanar da maka shugaban Amurka Donald Trump a gaban kotu domin kalubalantar tirsasawar da ya ke masa wajen ganin ya sayar da kadarorin sa a cikin kasar.

Talla

Sanarwar da kamfanin ya gabatar ta ce sun ruga kotu ne domin kalubalantar matakin da shugaba Trump ya dauka na hana shi aiki da kuma bukatar ganin ya sayar da kadarorin sa ga Amurkawa.

Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewar gwamnatin China na iya amfani da na’urorin kamfanin na TikTok wajen gano inda manyan jami’an gwamnati su ke da kuma aikata leken asiri.

Trump dai na ci gaba da fuskantar takun saka tsakaninsa da 'yan kasuwa da kasuwancin China da ke cikin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.