Amurka

Trump ya zargi Democrat da yunkurin tafka magudi a zaben Nuwamba

Gangamin Jam'iyyar Republican yayin tabbatar da Donald Trump a matsayin dan takararta a zaben Nuwamba.
Gangamin Jam'iyyar Republican yayin tabbatar da Donald Trump a matsayin dan takararta a zaben Nuwamba. REUTERS/Carlos Barria

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewar 'yan Jam’iyyar Democrat na shirin tafka magudi a zaben shugaban kasar da zai gudana cikin watan Nuwamba mai zuwa, zaben da Trump zai kara da Joe Biden.

Talla

Donald Trump wanda ke wannan zargi jim kadan bayan Jam’iyyarsa ta Republican ta kammala amincewa da takararsa karo na biyu a zaben shugaban kasar na watan Nuwamba, shugaban ya bayyana a wurin taron da ya gudana a Jihar North Carolina inda ya ce yana da shakku kan zaben mai zuwa.

Trump ya bukaci ‘ya'yan Jam’iyyar sa ta Republican su bude idanun su saboda abinda ya kira yunkurin 'yan Jam’iyyar Democrat na sace zaben wajen kara yawan masu kada kuri’u ta gidan waya.

Shugaban ya bayyana karara cewar, ''suna kokarin sace zaben, domin babu hanyar da zasu iya kada mu sai ta hanyar magudi''.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a na nuna cewa Joe Biden ke sahun gaba wajen shirin lashe zaben, yayin da Amurkawa ke cigaba da bayyana rashin amincewarsu da rawar da Trump ke takawa musamman wajen yaki da annobar COVID-19 da kuma matsalar tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.