WHO-Corona

Adadin wadanda coronavirus ta kashe ya zarce 820,000

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO. Fabrice Coffrini/Pool via REUTERS

Hukumar Lafiya ta Duniya tace adadin mutanen da annobar korona ta kashe sun zarce 820,000 a fadin duniya, daga cikin mutane kusa miliyan 24 da suka harbu da ita.

Talla

Hukumar tace har yanzu Amurka ke sahun gaba wajen samun mutanen da suka mutu sakamakon cutar, inda adadin su ya kai 178,524, sai Brazil mai 116,580, sannan Mexico mai mutane 61,450, sai India mai mutane 59,449 sannan Birtaniya mai mutane 41,449.

Wani sabon binciken masana ya ce ga alama mata na da sinadaren dake kare su daga kamuwa da cutar fiye da maza.

Yanzu dai haka cutar ta fara sake dawowa wasu kasashen da suka yi nasarar dakile ta, musamman kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.