Turkiya

Turkiya da Girka sun girke jiragen ruwan yaki kan tankiyar da ke tsakaninsu

Tankiyar dai ta karfafa ne bayan gano tarin iskar gas makale a karkashin yankin.
Tankiyar dai ta karfafa ne bayan gano tarin iskar gas makale a karkashin yankin. REUTERS

Zaman tankiya na ci gaba da kamari a yankin tekun Mediterranean, inda Turkiyya ke sa-in-sa da Girka da Tarayyar Turai a game da wanda zai yi iko da dimbim iskar gas da ke yankin batun da ya sanya bangarorin biyu girke dakarun Soji.

Talla

Tuni Jamus ta bukaci bangarorin biyu da su kwantar da hankulansu bayan da dukkaninsu suka fara jibge jiragen ruwa na yaki biyo bayan tankiyar da ke kokarimn juyewa zuwa rikicin yanki.

An fara wannan zaman tankiya ne a lokacin da Turkiya ta sanya hannu a wata yarjejeniya a watan Nuwamban 2019 da gwamnatin Libya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya wacce ta bayar da wani wagegen yankin Mediterranean ga Turkiya.

A watan Janairun 2020 kasashen Masar, Cyprus, Girka da Faransa sun caccaki yarjejeniyar, har ma da ta tsaro da Turkiya ta sanya hannu da gwamnatin Libya suna mai bayyana ta a matsayin wasa da cin gashin kansu.

Laluben da ake na makamashi a yankin ya dade da janyo rikici a tsakanin kasashen, kuma gano dimbim arzikin iskar gas a yankin ya matukar tayar da zalamar Turkiya.

A watan Yuni, Turkiyya ta nuna rashin amincewarta a game da duba wani jirgin daukar kaya da ake zargin yana jigilar makamai zuwa Libya da bangaren sojin Tarayyar Turai ta yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI