WHO

WHO na shirin sauya salon da ta ke amfani da shi wajen bayyana annoba

Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO.
Tedros Adhanom Ghebreyesus, shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO. Christopher Black/OMS/Handout via Reuters

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta kafa wani kwamiti da zai nazarci yadda za ta sauya salon da ta ke amfani da shi wajen bayyana annoba idan halin hakan ya taso sakamakon sukar da ya biyo bayan barkewar annobar COVID-19.

Talla

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus ya sanar da haka inda ya ke cewa cutar COVID-19 ta zama wani zakaran gwajin dafi ga kasashen duniya da kuma ita hukumar kan ta, abinda ya sa za ta sake nazari akai domin daukar matsayin gyara a inda ya dace.

Gebreyesus ya ce kafin bullar annobar COVID-19 an samu irin wannan matsalar lokacin da aka samu cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, abinda ke nuna cewar lokaci ya yi da za a yi wa tsarin gyaran fuska.

Kasashe da dama sun bukaci sake tsarin da hukumar ke bi wajen matakan bayyana annoba daga matakin kasa zuwa shiyya da kuma duniya baki daya.

Hukumar Lafiya ta gamu da mummunar suka daga Amurka kan bayyana bullar cutar korona, abinda ya kai ga shugaba Donald Trump ya janye kasar da kuma kudaden da ya ke bata a matsayin tallafi kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.