Faransa-Iraqi

Macron ya kai ziyarar farko zuwa Iraqi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin gaisawa da takwaransa na Iraqi Barham Saleh
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin gaisawa da takwaransa na Iraqi Barham Saleh Iraq Presidency/Handout via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya kammala ziyara aiki da ya kai a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi, inda ya gana da shugaban kasar da kuma Firaminista.

Talla

Macron ya jaddada fatan ganin an kawo karshen shisshigin da wasu kasashen yi a lamurran cikin gidan kasar ta Iraki.

A karshen ziyarar, shugaba Macron ya ce Faransa za ta taimaka wa Iraqi ta hanyar shirya wani gagarumin taro a birnin Paris da zai samu halartar Firaministan kasar a cikin wata daya mai zuwa.

A cikin kwanakin da za su biyo baya, kuma gwamnatin Faransar za ta sake zama domin duba irin ci gaban da gwamnatin da ke kan karagar mulki a Iraki ta samu, domin yanke shawara dangane da irin karin tallafin da za ta bai wa kasar.

Wani karin muhimmin batun kuma shi ne gina titin jirgin kasa na karkashin kasa a birnin Bagadaza da Faransar za ta taimakawa Iraqi wajen aiwatarwa, sai kuma bunkasa a fannin samar da makamashi, ilimi da kuma musayar al’adu a tsakanin kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.