Trump ya bukaci magoya bayansa da suka kada kuri'a sau 2

Shugaban Amurka Donald Trump yayin taron jam'iyyarsa ta Republican
Shugaban Amurka Donald Trump yayin taron jam'iyyarsa ta Republican CHIP SOMODEVILLA / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / Getty Images via

Shugaban Amurka Donald Trump, ya sabanta kiran da ya yi wa magoya bayansa cewa su kada kuri’a sau biyu a ranar 3 ga watan Nuwamba, yana mai cewa ta haka ne kawai za su samu tabbacin cewa an kidaya kuri’un nasu.

Talla

Trump ya bukaci Amurkawa da su fara kada kuri’arsu ta imel idan har akwai zabin yin haka a a yankunansu, sannan su nufi rumfar zabe su duba ko an kidaya, idan kuma aka samu akasi, su sake kadawa, yana mai cewa ta nan ne za su tabbatar an kidaya kuri’unsu.

Wannan ne suka ta baya bayan nan da shugaban ya yi a game da raunin amfani da imel wajen kada kuri’a, wanda hukumomi ke fadadawa a fadin kasar a matsayin wani mataki na kariya daga cutar coronavirus.

Sai dai duk da kushewa ba kakkautawa da Trump ya ke wa salon zabe ta imel, an riga an yi nisa wajen amfani da shi saboda ya bazu zuwa lungu da sako na kasar.

Yayin da shugaban na Amurka ke cewa wannan salon zabe zai bude kofar coge da cuwa – cuwa na kuri’u, kwararru na cewa ya zuwa yanzu babu wata shaida da ta tabbatar da haka.

Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin al’ummma na nuni da cewa jam’iyyar Democrats ke kan gaba a zabe ta hanyar Imel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.