Coronavirus

Adadin jami'an lafiyar da COVID-19 ta kashe ya haura dubu 7

Zuwa yanzu dai fiye da mutane dubu 860 cutar ta COVID-19 ta kashe a sassan duniya cikinw adanda suka kamu fiye da miliyan 27.
Zuwa yanzu dai fiye da mutane dubu 860 cutar ta COVID-19 ta kashe a sassan duniya cikinw adanda suka kamu fiye da miliyan 27. PEDRO PARDO / AFPPEDRO PARDO / AFP

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce akalla ma’aikatan lafiya dubu 7 suka kwanta dama sanadiyyar annobar COVID-19 a kokarin da su ke na ceto rayukan jama’a da kaso mai yawa na akalla jamai’an lafiyar dubu 1 da 300 a Mexico kadai.

Talla

Shugaban sashen tattali da tabbatar da adalci na kungiyar Steve Cockburn ya ce kowanne ma’aikacin lafiya na da cikakken ‘yancin samun kariya a aikinsa maimakon barinsu suna shiga hadarin da ke kai su ga asarar rayukansu.

Shugaban ya bayyana cewa, tun bayan barkewar cutar dama tsanantar ta a wata na ukun farkon shekarar nan, alkaluma na nuna yadda jami’an lafiyar ke rasa rayukansu musamman a Mexico, Brazil da Amurka yayinda tsanantar cutar a kasashen India da Afrika ta kudu ke sake sanya fargaba kan tsaron lafiyar jami’an.

Alkaluman Amnesty ya nuna cewa akwai ma’aikatan lafiya dubu 1 da 320 da coronavirus ta kashe Mexico sai wasu dubu 1 da 77 a Amurka kana wasu 649 a Birtaniya tukuna wasu jami’an lafiyar 634 a Brazil baya ga wasu 631 a Rasha da kuma wasu 573 a India.

Kungiyar ta Amnesty ta bayyana cewa da yiwuwar adadin jami’an ya zarce ko ma ninka alkaluman da ta ke da su la’akari da cewa kasashe da dama basa shigar da bayanai yadda ya kamata.

Zuwa yanzu dai fiye da mutane dubu 860 cutar ta COVID-19 ta kashe a sassan duniya cikinw adanda suka kamu fiye da miliyan 27.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.