Amurka

An soma kada kuri'a ta hanyar intanet a Amurka

Zabe ta hanyar Email a yankin Carollina na kasar Amurka
Zabe ta hanyar Email a yankin Carollina na kasar Amurka REUTERS/Mike Segar

A wasu yankunan Amurka ,yau ne yan kasar suka fara kada kuri’u su don bayyana zabin su ga mutumen da ya caccanci shugabantar kasar tsakanin Donald Trump da Joe Biden a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba tareda aikewa da kuri’ar su ta hanyar Intanet.

Talla

Arewacin Carolina ne aka soma da zaben inda ake sa ran aikewa da kusan takardun zabe dubu 600 .

Zaben dake zuwa kwanaki kalilan bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci Amurkawa da su fara kada kuri’arsu ta imel idan har akwai zabin yin haka a a yankunansu, sannan su nufi rumfar zabe su duba ko an kidaya, idan kuma aka samu akasi, su sake kadawa, yana mai cewa ta nan ne za su tabbatar an kidaya kuri’unsu.

Wannan ne suka ta baya bayan nan da shugaban ya yi a game da raunin amfani da imel wajen kada kuri’a, wanda hukumomi ke fadadawa a fadin kasar a matsayin wani mataki na kariya daga cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.