Amurka

Dumamar duniya za ta magance kanta-Trump

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sha karyata batun dumamar duniya
Shugaba Donald Trump na Amurka ya sha karyata batun dumamar duniya REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce dumamayar yanayi da duniya ke fama ita, matsala ce da za ta magance kanta da kanta, domin kuwa nan ba da jimawa duniyar za ta rikide zuwa sanyi a cewarsa.

Talla

Trump, wanda ya ziyarci yankin California da yanzu haka ke fama da wutar daji wadda ta kashe mutane akalla 31, ya yi watsi da zargin da abokin hamayyarsa na siyasa Joe Biden ya yi da ke danganta gobarar da dumamar yanayi.

Shugaba Trump ya nanata cewa, rashin kyakkyawar kulawa da dazuka ne ya haddasa ibtila’in wutar dajin na baya-bayan, yayin da ya gana da zaratan jami’an tsaron da ke yaki da gobarar dajin a California don jinjina musu.

Trump ya sha karyata batutuwan da suka danganci matsalar sauyin yanayi duk da hujjojin da masana kimiya ke gabatarwa.

A bangare guda Mista Biden ya ce, muddin Trump ya yi tazarce don karin wa’adin shekaru hudu nan gaba a fadar White House, hakan zai dada jefa Amurka cikin bala’o’in wutar daji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.