Amurka

Za mu rubanya hare-hare kan Iran-Trump

Donald Trump
Donald Trump David T. Foster/Reuters

Shugaba Donald Trump ya lashi takobin rubanya harin ramuyar gayya sau dubu guda kan Iran wadda ke shirin daukar fansar kisan da Amurka ta yi wa babban kwamandan sojinta Janar Qasem Soleimani kamar yadda rahotanni ke cewa.

Talla

Rahotanni daga kafafen yada labaran Amurka sun ce, kasar Iran na kitsa yadda za ta kashe jakadiyar Amurka a Afrika ta Kudu kafin gudanar da zaben shugaban kasa na watan Nuwamba wanda za a fafata tsakanin Trump da Joe Biden.

Sai dai shugaba Trump ya ce, muddin Iran ta yi gigin far wa Amurka ta kowacce hanya, to babu shakka za ta dandana kudarta.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ki cewa uffam kai tsaye game da rahotannin barazanar kashe Lana Marks da ke zama jakadiyar Amurka a Afrika ta Kudu. Marks na da kusanci sosai da shugaba Trump.

Amma Pompeo ya ce, suna daukar wannan barazana da muhimmancin gaske.

Gwamnatin Iran ta musanta wannan zargi, tana mai cewa, wani yunkuri ne na bata mata suna a idon kasashen duniya.

Tsamin dangantaka ya tsananta tsakanin kasashen biyu tun bayan da Trump ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen dunya.

A cikin watan Janairu ne, jirgin Amurka mara matuki ya kashe Soleimani a birnin Bagadaza, sannan kuma Amurka na yunkurin tsawaita takunkumin hana cinikayyar makamai da Iran duk da cewa zai kawo karshe a cikin watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.