Amurka

Sally dauke da ruwan sama mai karfi ta afkawa jihohin Alabama da Florida

Guguwar da ta afkawa yankunan Amurka
Guguwar da ta afkawa yankunan Amurka Mouche/RFI

Guguwar Sally dauke da ruwan sama mai karfi ta afkawa yankunan gabar ruwa dake jihohin Alabama da kuma Florida, inda yanzu haka jami’an agaji ke fafutukar ceto jama’a daga halaka a ambaliyar ruwa.

Talla

Cibiyar kwararru kan yanayi ta NHC a Amurka tace guguwar ta Sally, ta isa yankunan jihohin Florida da Alabama ne da kusan karfe 5 na safiyar yau Laraba cikin gudun kilomita 165 a sa’a 1.

Masanan sun kuma yi gargadin cewa guguwar ta Sally ka iya haifar da mummunar ambaliyar da aka share shekaru ba a ga irinta ba a yankunan da ta afkawa la’akari da yawan ruwan saman da take dauke da shi mai zurfin akalla inci 20 idan ya sauka doron kasa.

Kawo yanzu dai kakkarfar guguwar ta katse lantarkin sama da gidaje dubu dubu 500, bayaga tumbuke bishiyoyi masu yawan gaske.

Ranar Litinin gwamnan jihar Alabama Kay Ivey ya kafa dokar ta baci kafin zuwan tun kafin zuwan guguwar da Sally.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.