ICC-Isra'ila

ICC ta yi watsi neman bincikar Isra’ila kan farmakin 2010 a Gaza

Jirgin ruwan agajin Mavi Marmara da Isra'ila ta kaiwa farmaki a shekarar 2010.
Jirgin ruwan agajin Mavi Marmara da Isra'ila ta kaiwa farmaki a shekarar 2010. Wikipedia / Free Gaza movement

Kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya ICC, ta yi watsi da bukatar da aka shigar a gabanta, dake neman a binciki Isra’ila a game da farmakin da ta kai wa wani jirgin ruwan agaji a kan hanyarsa ta isa zirin Gaza a shekara ta 2010.

Talla

A lokacin wannan farmaki da dakarun Isra’ila suka kai kan wannan jirgi da ke dauke da kayayyakin jinkai, ‘yan asalin kasar Turkiyya 9 ne suka rasa rayukansu nan take, yayin da mutum na 10 ya rasa rayuwarsa daga bisani.

Tun cikin watan disambar da ya gabata mai shigar da kara ta kotun Duniya Fatou Bensouda, ta bayyana cewa ba wasu cikakkun hujjar sake bude bincike a game da zargin cewa Isra’ila ta aikata laifin.

Tun a wancan lokaci, kasar Comoro inda aka yi wa jirgin ruwan agajin rijista mai suna Mavi Marmara, ta yanke shawarar shigar da kara gaban kotun ta duniya don nuna rashin amincewa da hukunci farko da kotun ta yanke.

Duk da cewa a hukuncin da ta yanke a wannan laraba kotun ta ce akwai wasu ‘yan kura-kurai a cikin hukuncin farko da aka yanke shekara ta 2014, tace kura-kuran basu kai a soke hukuncin farkon ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI