Duniya

An bukaci attajiran duniya su ciyar da miliyoyin talakawa

Talakawa miliyan 270 ke fama da matsananciyar yunwa a sassan duniya
Talakawa miliyan 270 ke fama da matsananciyar yunwa a sassan duniya RFI/Alexis Guilleux

Shugaban Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya David Bearsley ya bukaci attajiran duniya da su tashi tsaye wajen ceto rayukan mutane akalla miliyan 30 da ke fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwa. 

Talla

Bearsley ya shaida wa Kwamitin Sulhu cewa, yanzu haka mutane miliyan 270 ke fuskantar yunwa a duniya, amma kuma miliyan 30 daga cikinsu sun kai wani yanayi na tada hankali.

Jami’in ya ce suna bukatar akalla Dala biliyan 5 domin ciyar da mutane miliyan 30 a shekara guda, saboda haka suke bukatar taimakon atttajiran duniya sama da  dubu 2 da su taimaka wajen ganin sun samu nasarar kai dauki ga mutane akalla miliyan 138.

Bearsley ya ce, a cikin makwanni 11 daga ranar 18 ga watan Maris da aka fara killace Amurkawa sakamakon barkewar annobar korona, arzikin Jeff Bezos da ya mallaki kamfanin Amazon ya karu da sama da Dala biliyan 36, yayin da Mark Zuckerberg ya samu karin sama da Dala biliyan 30 kan arzikinsa, sai kuma Elon Musk mai kamfanin Tesla da ya samu karin sama da Dala biliyan 14.

Shugaban hukumar ya ce, ya zama tilas wadannan attajirai su taimaka wa matalauta a cikin irin wannan yanayi da suka samu kansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.