Afrika

Hafsoshin tsaron Amurka da Faransa sun gana kan Afrika

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da dakarun kasar a Jamhuriyar Nijar
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da dakarun kasar a Jamhuriyar Nijar LUDOVIC MARIN / AFP

Babban Kwamandan Sojin Amurka a yankin Afrika ya gana da babban hafsan tsaron Faransa domin tattaunawa kan yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda a Afrika a daidai lokacin da ake dari-darin cewa, shugaba Donald Trump ka iya janye dakarun da Amurka ta girke a nahiyar.

Talla

Babban Kwamadan Sojin Amurka a Afrika, Janar Stephen Townsend ya gana da babban hafson tsaron Faransa Janar Francois Lecointre game da kaddamar da wani aiki karkashin kawancen da ke tsakanin kasashen biyu a Afrika.

Amurka ta taimaka wajen bai wa jiragen yakin Faransa mai a sararin samaniya, baya ga agaza mata wajen musayar bayanan sirri a yayin yaki da ‘yan ta’adda a kasashen yammacin Afrika, inda mayakan jihadi suka dasa tushensu.

Sanarwar da Amurka ta fitar ta ce, bayanan sirrin da Amurka ta tattara, sun taimaka wa dakarun Faransa wajen kashe shugaban Kungiyar Al-Qaeda a yankin Maghreb wato, Abdel Malik Droukdel a cikin watan Yuni.

Sai dai a halin yanzu, gwamnatin shugaba Donald Trump ta hakikance cewa, dole ne ta mayar da hankali kan kasashen Rasha da China, lura da cewa, tana kallon Afrika a matsayin barazanar da ba ta taka kara ta karya ba, a don haka take tunanin janyewa daga nahiyar don kyale Faransa da Kungiyar Turai su kadai a nahiyar.

Faransa na da fiye da dakaru dubu 5 karkashin rundunar Barkhane da ke yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.