WHO

Coronavirus ta lakume rayuka kusan dubu 50 a mako 1 - WHO

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana kaduwa kan karuwar adadin mutanen da annobar coronavirus ke halakawa a sassan duniya, wadda tace sabbin alkalumanta sun nuna cewar, kusan rayuka dubu 50 cutar ta lakume a mako 1.

Talla

Yanzu haka dai akalla mutane dubu 948 annobar ta kashe a fadin duniya, daga cikin akalla mutanen miliyan 30 da dubu 200 da suka kamu da cutar, tun bayan bullarta daga China a watan Disambar bara.

Yayin ganawa da manema labarai a jiya Juma’a, daraktan sashin ayyukan gaggawa na hukumar lafiyar ta duniya WHO Michael Ryan, yayi gargadin cewa har yanzu akwai jan aiki gaban hukumomin kasashe wajen yaki da annobar ta coronavirus, wadda a yanzu haka ke sake barkewa karo na biyu, a sassan duniya musamman a nahiyar Turai, bayan saukin da aka samu a ‘yan makwannin baya.

Sake barkewar annobar ta coronavirus a sassan Turai, ya sanya hukumomin wasu kasashen nahiyar daukar matakan sake killace wasu daga cikin yankunansu.

A Spain, hukumomin kasar sun bada umarnin killace akalla kashi 13 cikin 100 na al’ummar dake Madrid babban birnin kasar, sakamakon sake yaduwar da cutar ke yi cikin gaggawa.

A Birtaniya kuwa, gargadi gwamnati ta yi kan yiwuwar sake killace daukacin al’ummar kasar a gidajensu, la’akari da ninkawa sau biyu na adadin wadanda cutar ta coronavirus ke tilasta garzayawa da su asibiti.

Sai kuma Faransa dake shirin fitar da sabbin tsare-tsaren matakan yakar annobar da tace a wannan karon gwamnatocin yankunan da kananan hukumomi ne za su aiwatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.