Fitattun mutane na ci gaba da alhinin mutuwar shugabar kotun kolin Amurka
Wallafawa ranar:
Fitattun mutane na ci gaba da mayar da martani kan rasuwar shugabar kotun kolin Amurka, mai shari’a Ruth Bader Ginsburg wadda ta rasu tana da shekaru 87 a duniya.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana marigayiyar Ginsburg a matsayin wadda ta taka gagarumar rawa wajen tabbatar da ‘yancin mata da samun daidaito tare da kare hakkin Bil Adama.
Tsohon shugaban kasar Barack Obama ya bayyana Ginsburg a matsayin wadda ta yi ta gwagwarmayar tabbatar da dorewar dimokiradiya da bin doka da oda a Amurka.
Dan takaran Jam’iyyar Democrat Joe Biden ya bayyana marigayiyar a matsayin tauraruwar Amurka da kuma wani ginshiki wajen tabbatar da gaskiya a bangaren shari’a.
Babban mai shari’a a kotun Koli John Roberts ya ce Amurka ta yi asarar mai shari’ar da ta kafa tarihi.
Yanzu haka daruruwan Amurka cikin hawaye na cigaba da aje firanni a gaban kotun kolin domin nuna alhinin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu