Iran-Amurka

Iran ta nanata aniyar farmakar masu hannu a kisan Qasem Soleimani

Hoton babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qassem Soleimani da Amurka ta yiwa kisan gilla.
Hoton babban kwamandan Sojin Iran a ketare Qassem Soleimani da Amurka ta yiwa kisan gilla. REUTERS/Naif Rahma

Kwamandan Zaratan sojin iran Hossein Salami ya sha alwashin kai hari kan duk wadanda su ke da hannu wajen hallaka Janar Qasem Soleimani da Amurka ta kashe a harin da ta kai Iraqi a watan Janairu.

Talla

Shafin intanet na sojin Iran ya ruwaito Janar Salami na shaidawa shugaba Donald Trump cewar ramakon su kan shahadar da fitaccen Janar din ya yi babu tantama a ciki, kuma yana nan tafe.

Shugaba Donald Trump a cikin wannan mako ya yi gargadin cewar Amurka za ta mayar da gagarumin martani kan duk wani mataki na Iran da ya shafi yunkurin daukar fan sa kan kisan da aka yiwa Janar Qassem Soleimani, inda ya ke cewa idan sun kai mana hari ta kowanne fanni, mun bada umurni a rubuce akai musu irin sa har sau dubu.

Gargadin Trump na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta yi zargin cewar Iran na kokarin kashe Jakadiyar kasar da ke Afirka ta kudu Lana Marks zargin da hukumomin Afirka ta kudu suka ce babu gaskiya a cikin sa.

Janar Salami ya ce ba za su kai wa Jakadiyar mace hari ba, sai dai za su kaiwa duk wadanda su ke da hannu wajen kashe Janar Qasem Soleimani, kuma duk wanda ya ke da hannu a ciki ya saurari hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.