Muhalli

Kashi 68 na nau'ikan dabbobi, kifaye da tsirrai sun bace daga doron kasa - Kwararru

Ayyukan dan adam na kara haifar da mummunar illa ga muhallinsa.
Ayyukan dan adam na kara haifar da mummunar illa ga muhallinsa. REUTERS/David Gray

Manyan kungiyoyi gami da hukumomin dake wakiltar miliyoyin mutane a sassan duniya, suka fitar da sanarwar hadin gwiwa da ta bukaci gwamnatocin kasashe da su gaggauta daukar matakan kawo karshen gurbacewar muhalli da sauyin yanayi, wadanda barnar dan adam ke haddasawa.

Talla

Wanna sabon yunkuri ya zo ne a daidai lokacin da kwararru a kimiyya ke gargadin cewa ayyukan dan adam na kara haifar da mummunar illa ga muhallinsa.

Rahoton bayan bayan nan da masanan suka wallafa kan halin da duniya ke ciki, yayi gargadin cewa gurbacewar yanayi da muhalli na kara yin muni cikin gaggawa sama da kowane lokaci a tarihin rayuwar dan adam, inda suka ce a yanzu haka akalla nau’o’in halittu miliyan 1 ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa nan da ‘yan shekaru, saboda matsalar ta gurbacewar muhalli.

A makon jiya ne kuma asusun baiwa muhalli kariya na duniya WWF yace bincikensa ya gano cewar kashi 68 cikin 100 na dangogin namun daji, tsuntsaye, kifaye da kuma nau’ikan tsirrai sun bace daga doron kasa daga shekarar 1970 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI