Amurka-Iran

Nukiliya: Amurka tayi gaban kanta wajen sake laftawa Iran takunkumai

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo Mike Segar/Reuters

Cikin yanayi na bazata Amurka ta yi gaban kanta wajen sanar da sake laftawa Iran dukkanin takunkuman karya tattalin arzikin da aka taba kakaba mata a shekarun baya, wadanda daga bisani majalisar dinkin duniya janye su bayan cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyarta da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Talla

Amurka ta yi wannan ikirari ta hannun sakataren harkokin wajenta Mike Pompeo, wanda yace dukkanin takunkuman da a baya Amurka ta jagoranci kakabawa kasar ta Iran kan shirinta na nukiliya sun koma aiki daga karfe 8 na daren ranar asabar 19 ga watan Satumba.

Masu sharhi dai na ganin babu shakka matin Amurka zai sake dagula lamurra ne tsakaninta da Iran, wadda dama tuni dangantakarsu tayi tsami, bayan da a shekarar 2018, shugaba Trump ya janye da yarjejeniyar nukiliyarta ta 2015, tare da kakaba mata wasu takunkumai, wanda manyan kasashe Turai ciki har da Birtaniya, Jamus da Faransa suka bijirewa.

Tun bayan ficewar Amurka daga cikin yarjejeniyar, Iran ta soma bijire mata, ta hanyar kara matakan shirin nukiliyarta na tace makamashin Uranium, abinda a yanzu ake fargabar zai ma iya zarta hakan, idan har Iran din ta yiwa Amurka raddi mai zafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.