Amurkaa-Iran

Amurka ta zama saniyar ware a duniya-Iran

Shugaban Iran Hassan Rohani.
Shugaban Iran Hassan Rohani. REUTERS/Brendan McDermid

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya yi ikirarin cewa yanzu haka Amurka na matsayin saniyar ware tsakanin manyan kasashen Duniya, dangane da bukatar da ta mika gaban Majalisar Dinkin Duniya na ganin an sabunta takunkuman karya tattalin arzikin da ke kan Tehran.

Talla

A jawabinsa ta gidan talabijin Hassan Rouhani ya ce ga alama, matsin lambar Amurka na ganin an sake kakaba wa Iran takunkumai, ya juye zuwa matsi gare ta na zamowa saniyar ware tsakanin takwarorinta bayan da suka juya baya ga bukatarta gaban Majalisar Dinkin Duniya na ganin lallai an sabunta takunkuman da ke kan kasar duk da ficewarta daga yarjejeniyar nukiliyar Iran din da kasashen duniya ta 2015.

Shugaba Donald Trump na Amurka ne dai ya tsaya kai da fata wajen ganin, Majalisar ta sahale sabunta takunkuman kan Iran batun da sauran kasashen da ke cikin yarjejeniyar su ka yi biris da shi, yayin da yanzu haka ta ke ci gaba da barazanar daukar mataki kan duk kasar da ta ki goyon bayanta kan batun.

Bayan barazanar ta Amurka, kasashen Faransa  da Jamus da Birtaniya sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ke matsayin martani inda suke cewa babu ta yadda za ta iya daukar mataki kan bijirewar ta su, yayin da Rasha a wata sanarwa ta daban ta ce Amurka ba ta da wani hurumi a shari’ance da zai ba ta damar daukar matakin.

A jawabin na Rouhani ya yaba wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi watsi da bukatar ta Amurka, yana mai cewa matukar kasashen da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta Iran suka aminta da ba ta damar ci gaba da cin gajiyar sassaucin tattalin arzikin da yarjejeniyar ta kunsa, Tehran a shirye ta ke ta yi watsi da matakan da ta dauka na habaka sashen nukiliyarta bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.