Tattalin Arziki

Manyan bankunan duniya na da hannu a kudaden sata

Ginin bankin HSBC
Ginin bankin HSBC PHILIPPE LOPEZ / AFP

Wani bincike ya bankado cewar katafaren Bankin HSBC da wasu bankuna 4 na duniya sun taka rawa sosai wajen halarta kudaden haramun da safarar makudan kudaden sata da na cinikin kwaya a fadin duniya.

Talla

Binciken da tawagar 'yan jaridun da ke bin kwakwaf da kamfanin Buzzfeed suka gudanar ya nuna cewa, bankin ya bada dama wajen sarrafa kudaden da aka samu wajen cinikin kwaya a kasashen da ake yaki da kudaden da shugabannin suka sace daga kasashe masu tasowa da kuma kudaden ajiyar mutane da ake sacewa a bankuna, duk da korafin da wasu daga cikin ma’aikatan bankin ke yi.

Binciken da kafofin yada labaran duniya 108 suka sanya hannu a ciki daga kasashe 88 ya biyo bayan dubban zarge-zargen da bankuna suka gabatar wa Baitulmalin Amurka da na kasashen Turai.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa, bankin HSBC tare da wasu bankuna 4 ya taimaka wajen halarta kudaden haramun da suka kai Dala tiriliyan 2 tsakanin shekarar 1999 zuwa 2017.

Sauran bankunan da ake zargin suna da hannu dumu dumu wajen wannan badakala ta taimaka wa barayi sun hada da JP Morgan Chase da Standard Chartered da Deutsche Bank da Bankin New York Mellon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.