UN

MDD na bikin cika shekara 75

Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a bara
Zauren taron Majalisar Dinkin Duniya a bara UN Photo/Loey Felipe

A yau Litinin Majalisar Dinkin Duniya ke bikin cika shekaru 75 da kafuwa, inda take jaddada mahimancin hadin-kai a tsakanin kasashe a daidai lokacin da annobar coronavirus ta raunata dangantakar da ke tsakanin kasashe.

Talla

Za a fara wannan bikin ne da babban taron Majalisar Dinkin Duniya na shekara shekara, inda bisa al’ada, jagorori da wakilai daga kasashen duniya kusan 200 za su gabatar da jawabai don jaddada mataslolin da ke addabar duniya da zummar lalubo mafita.

Sai dai a wannan shekarar ba za a garkame wani bangare na birnin Manhanttan kamar yadda aka saba ba duk lokacin da ake wannan babban taro, sannan kuma ba za a ga jerin gwanon motocin kasaita ba da kuma kai kawo na jami’an diflomasiya da ‘yan jarida da kuma masu tafinta a zauren Majalisar.

Wannan kuwa na faruwa ne sakamakon matakan da ake dauka na dakile cutar COVID 19, inda aka takaita zirga-zirga da cudanya a fadin duniya, wakili daya kacal aka yarje wa kowacce kasa daga cikin kasashe 193 da ke cikin majalisar ta aike taron, kuma shi din ma sai idan yana cikin Amurka a halin da ake ciki, sauran wakilan kuma sai dai a dama da su ta majigin bidiyo.

A ranar Talata shugaban Rasha Vladimir Putin da na China Xi Jinping da ma na Amurka Donald Trump, za su gabatar da jawabinsu a taron ta kafar bidiyo.

Sai kuma ranar Laraba, shugaban Venezuela, Nicolas Maduro wanda wani bangare na duniya ke wa gwamnatinsa kallon haramtacciya zai yi jawabi ta bidiyo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.