MDD

MDD ta fara babban taron zaurenta ba tare da mahalarta ba

Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na 2019.
Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na 2019. REUTERS/Shannon Stapleton

Majalisar Dinkin Duniya ta fara taron babban zauren ta na shekara-shekara a yau Talata, taron da zai tattauna kalubalen da suka dabaibaye duniya sanadiyyar annobar Covid-19 ko da ya ke a wannan karon taron ya zo da wani salo sabanin yadda aka saba gani bisa al’ada.

Talla

Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniyar wanda bisa al’ada ke karbar bakoncin mahalarta kusan dubu 10 daga sassan duniya kama daga shugabanni jami’an Diflomasiyya da kuma kwararru a fanoni daban-daban, don tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi mu’amalar kasashe tattalin arziki da kalubalen da duniyar ke fuskanta don warwarewa, a wannan karon na gudana ne ba tare da mahalarta daga kowacce kasa ba a yau Talata.

Maimakon halartar shugabannin gaban zauren don gabatar da jawabi, a wanann karon kowannensu zai aike da sakon jawabinsa ne ta Internat, ta yadda za a kunna shi ga sauran shugabannin da suma za su aiko da nasu don tattaunawa kansa, ko da ya ke kowacce kasa za ta aike da jami’in Diflomasiyya guda zuwa zauren majalisar amma fa karkashin matakan kariya daga Covid-19 da ke ci gaba da kisan jama’a.

Taron babban zauren na Majalisar Dinkin Duniya bai bayar da damar kebantacciyar tattaunawa kamar yadda aka saba kowacce shekara ba, sai dai yayin ganawar bidiyon intanet tsakanin shugabannin za su tattauna kan matsalolin da suka shafi annobar Covid-19, dumamar yanayi, gurbacewar muhalli da kai ga bacewar wasu halittu a ban kasa, baya ga rikicin siyasar Libya da na Lebanon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.