Adadin Mutanen da annobar korona ta kashe a Amurka ya zarce dubu 200

Shugaban Amurka Donald Trump yayin kallon taswirar korona a kasar
Shugaban Amurka Donald Trump yayin kallon taswirar korona a kasar REUTERS/Leah Millis

Adadin Mutanen da annobar korona ta kashe a kasar Amurka ya zarce dubu 200 a daidai lokacin da kasar ke fuskantar zaben shugaban kasa mai zafi tsakanin shugaba Donald Trump da abokin karawar sa Joe Biden.

Talla

Jami’ar Johns Hopkins dake tattra alkaluman masu dauke da cutar, tace ya zuwa jiya an samu mutane 200,182 da suka mutu a fadin Amurka, daga cikin mutane kusan da miliyan 7 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Yanzu haka Amurka ke matsayi na farko na yawan mutanen da suka mutu, sai Brazil mai mutane 133,272 sannan India mai mutane 88,935.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.